<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>196</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Yesu, Ruhunka kaɗai zai juye zuciyarmu,
 Ikonsa ma a cikinmu zai sake halinmu.

[V2]
 KORUS
 Ya Ruhu mai taimako, wurinmu duk ka zo,
 Ka cika dukan zuciyarmu, ka ba mu ikonka yau.

[V3]
 2) Ya Yesu, Ruhunka kaɗai, zai ba mu ƙaunarka,
 Ikonsa cikin ranmu kuwa zai juye gurinmu.
 Korus

[V4]
 3) Ruhunka, Yesu, ƙauna ne, Ruhun bangaskiya kuwa.
 Shi fid da kwaɗayinmu duk da ikon ƙaunarsa.
 Korus

[V5]
 4) Ya Ruhun Yesu, muna so ka ji addu'armu,
 Ka sauko nan da ikonka, ka zauna bisanmu.
 Korus</lyrics>
<title>Ya Yesu, Ruhunka Kaɗai Zai Juye Zuciyarmu LW196</title>
</song>